Labarai
Har Yanzu Muna Ci Gaba Da Yajin Aiki — Ma’aikatan jinya

Kungiyar Ma’aikatan jinya da Ungozoma ta Ƙasa (NANNM) ta mayar wa da gwamnati martanin cewa har yanzu tana ci gaba da gudanar da yajin aikin da take yi.
Ministan Lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Ali Pate, ne dai ya bayyana cewa ƙungiyar ta janye yajin aikin gargaɗin.
Da yake magana da manema labarai bayan wani taron sirri da aka yi a Abuja ranar Juma’a, Pate ya ce matakin ya biyo bayan yarjejeniyoyin da gwamnati da shugabannin Ƙungiyar NANNM suka cimma ne.
Amma da aka tuntuɓi shugaban Ƙungiyar na ƙasa, Morakinyo Rilwan ya ce ba gaskiya ba ne cewa an janye yajin aikin.
“Idan har Ministan ne ya shirya yajin aikin, to zai iya janye yajin aikin, a ɓangarenmu yajin aikin da ƙungiyar ta shirya yana ci gaba da gudana, Ministan bai shirya yajin aikin ba, don haka ba shi da hurumin janye yajin.
Rilwan ya shaida wa Daily Trust ta wayar tarho cewa, “Akwai hanyoyin da za a bi, idan za a janye yajin aikin gaba ɗaya.
A ranar Laraba ne ma’aikatan jinya suka fara yajin aikin gargaɗi na kwanaki bakwai a faɗin ƙasar. Yajin aikin, a cewar shugabancin NANNM zai magance matsalolin da suka haɗa da rashin biyan albashi, ƙarancin ma’aikata, alawus-alawus da ba a biya ba da kuma rashin yanayin aiki mai kyau.
Wannan yajin aikin dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun takun saƙa tsakanin likitoci da gwamnati kan walwala da sauran batutuwa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Yajin aikin ma’aikatan jinya da ya biyo bayan cikar wa’adin kwanaki 15 da NNNM ta bai wa gwamnatin tarayya wanda ya kawo cikas ga harkokin kiwon lafiya a faɗin Najeriya.
-
Labarai6 days ago
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Yi Wa Masu Digirin Ƙasashen Waje Jarrabawa
-
Labarai2 days ago
Jami’an Tsaro A Pakistan Sun Kama ’Yan Najeriya 20 Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
-
Labarai1 day ago
Hare-haren Ta’addanci Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 835 A Najeriya Cikin Wata Guda – Rahoto
