News
Rundunar Sojin Ruwa Za Ta Kafa Sabon Sansani A Kebbi
Rundunar Sojin Ruwan Najeriya ta bayyana shirinta na kafa sansani a garin Yauri da ke Jihar Kebbi, a wani yunkuri na faɗaɗa tasirinta da kuma ƙarfafa matakan tsaron ruwa da iyakokin ƙasa.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ta biyo bayan ziyarar da wata tawagar manyan jami’an rundunar ta kai gidan gwamnatin jihar a ranar Alhamis.
Tawagar, ƙarƙashin jagorancin Rear Admiral Patrick Nwatu – wanda ya wakilci Babban Hafsan Sojin Ruwa na ƙasa – ta bayyana cewa rundunar na ƙoƙarin kafa sansanin ne domin tabbatar da tsaro a yankin kogin Niger da kewaye.
Rear Admiral Nwatu ya bayyana cewa kogin Niger, duk da mahimmancinsa ga noma, kamun kifi da samar da wutar lantarki, ya fara fuskantar barazana daga wasu miyagun ƙungiyoyi da ke amfani da hanyoyin ruwa wajen aikata laifuka.
“Mun lura da yadda wasu bata-gari ke amfani da wannan kogi wajen safarar makamai, miyagun ƙwayoyi da sauran ayyukan ta’addanci. Don haka muna ganin buƙatar sa ido da kafa sansani a yankin na da matuƙar muhimmanci,” in ji Nwatu.
Ya ce wannan mataki na daga cikin dabarun rundunar na faɗaɗa ayyukanta da kuma samar da tsaro mai ɗorewa, musamman a yankunan da ke da tasirin hanyoyin ruwa.
Gwamnatin Jihar Kebbi ta bayyana cewa tana maraba da wannan yunkuri, tare da tabbatar da cewa za ta bayar da haɗin kai don ganin aikin ya samu nasara.
Haka kuma, gwamnatin ta bayyana cewa kafa wannan sansani zai ba da damar buɗe ƙarin hanyoyin sadarwa da tattalin arziƙi a yankin, tare da taimakawa wajen magance matsalolin tsaro da ke addabar kogin.
