Connect with us

News

Ambaliya Ta Lalata Gidaje, Makarantu Da Gonaki A Bauchi, Filato Da Neja

Published

on

Ambaliya Ta Lalata Gidaje, Makarantu Da Gonaki a Bauchi, Filato da Neja

Ambaliya mai ƙarfi ta mamaye wasu yankuna a jihohin Bauchi, Filato da Neja, inda ta lalata gidaje, makarantu, wuraren ibada da gonaki, lamarin da ya tilasta wa ɗaruruwan mutane kaurace wa muhallansu.

Rahotanni sun nuna cewa ruwan saman da ya zubo da tsananin iska da karfi tun daga safiyar ranar Lahadi, ya tumbuke bishiyoyi da turakun lantarki, tare da yage rufin gine-gine da dama a yankunan da abin ya shafa.

WAEC Ta Saki Sakamakon Jarabawar 2025

A jihar Filato, rahoton DAILY TRUST ya bayyana cewa fiye da gine-gine 50 ne suka rushe a garin Menkaat, ƙaramar hukumar Shendam, sakamakon ƙarfafar ambaliya da aka fuskanta a yankin.

A jihar Bauchi kuwa, fiye da magidanta 40 a ƙaramar hukumar Dass sun rasa matsugunansu, baya ga dimbin gonakin da ambaliya ta lalata a sassa daban-daban na yankin.

Haka zalika a jihar Neja, rahotanni sun tabbatar da cewa akalla garuruwa 18 a ƙaramar hukumar Lapai ne suka fuskanci ambaliya, inda ruwa ya mamaye gonaki masu yawa tare da barazana ga rayuwar mazauna yankunan.

Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da Hukumar Kula da Yanayi ta Kasa (NiMet) ke ci gaba da bayar da gargadi kan yiwuwar samun ruwan sama mai yawa haɗe da ambaliya a wasu sassan ƙasar nan, musamman a watannin da suka rage kafin ƙarshen damina.

Advertisement

Masu ruwa da tsaki sun bukaci gwamnati ta gaggauta ɗaukar matakan tallafa wa waɗanda ambaliya ta shafa, tare da gyara hanyoyin ruwa da shimfiɗa dabarun dakile irin wannan iftila’i a gaba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending