News
Hatsarin Jiragen Ruwa Ya Lakume Rayuka Akalla 108 a Sakkwato Cikin Shekaru Biyar
Daga shekarar 2020 zuwa yanzu, Jihar Sakkwato ta yi asarar rayuka akalla 108 sakamakon hatsarin jiragen ruwa da aka samu sau takwas a kan kogunan jihar.
Rahotanni sun nuna cewa Najeriya gaba ɗaya ta rasa rayuka sama da 1,600 a hatsarin jiragen ruwa tsakanin 2020 da 2025.
Hatsarin baya-bayan nan shi ne wanda ya auku a ranar Lahadi, 17 ga watan Agusta, lokacin da jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji 51 ya kife a yankin Kojiyo, Karamar Hukumar Goronyo. An ceto mutane 25, yayin da 26 ake ci gaba da nema.
Jerin Manyan Hadurra a Sakkwato (2020 – 2025)
Agusta 2020 – Birjingo, Goronyo: Mutane 9 sun mutu, da dama sun tsira bayan jirgi ya kife da su a hanyar zuwa gonar shinkafa.
Yuni 2021 – Shagari: Mutane 13 sun mutu a hanyar Doruwa-Ginga.
Afrilu 2022 – Gidan Magana, Shagari: Mutane 29 sun mutu, ciki har da yara da wata amarya.
Mayu 2023 – Dandeji, Shagari: ’Yan mata 15 sun mutu, fasinjoji da dama sun bace.
Agusta 2024 – Dundaye, Wamakko: Mutane 4 sun mutu, 1 ya bace.
Disamba 2024 – Tangwale, Dundaye: Mutum 1 ya mutu, 34 aka ceto.
Yuni 2025 – Rinaye, Shagari: Mutane 7 sun mutu, ciki har da yara da mata aure.
Agusta 2025 – Kojiyo, Goronyo: Akalla ’yan kasuwa 30 sun mutu, wasu 26 sun bace.
A shekarar 2024, Gwamnatin Sakkwato ta ware Naira biliyan 1.1 don siyan jiragen ruwa masu injin, rigunan kariya da kayan agaji domin raba wa kananan hukumomin da ambaliya ta fi shafa.
Haka kuma, bayan hatsarin Agusta 2024, Gwamna Ahmed Aliyu ya bayar da tallafin Naira miliyan 30 ga iyalan waɗanda suka mutu da kuma waɗanda suka tsira.
Hukumar HYPPADEC ta bayyana cewa hatsarin jiragen ruwa ya kashe mutane 350 a Najeriya a shekarar 2020 kadai. Binciken Hukumar Binciken Hadurra ta Najeriya (NSIB) ya nuna cewa kashi 90% na mutanen da suka mutu a irin waɗannan hadurra ba su sanya rigar kare rai ba.
2020: Mutane 350 sun mutu
2021: Mutane 281 sun mutu, ciki har da 156 a Warrah, Kebbi
2022: Mutane 313 sun mutu
2023: Sama da 300 sun mutu
2024: Mutane 326 sun mutu, Niger da Kwara sun fi yawan mace-mace
2025 (har zuwa Yuli): Mutane 34 sun mutu
Shugaban HYPPADEC, Hon. Joseph Terfa Ityav, ya danganta hatsuran da cika da kaya, lalacewar jiragen ruwa, rashin rigunan kariya da kuma itatuwan da ke cikin koguna.
