News
Gwamna Namadi Ya Sallami Mai Ba Shi Shawara Na Musamman
Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya sallami mai ba shi shawara na musamman kan harkokin Majalisar Dokoki ta Kasa, Alhaji Rabi’u Garba Kaugama.
A wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Bala Ibrahim, ya fitar a ranar Talata, an bayyana cewa korar ta fara aiki nan take, duk da cewa ba a fayyace dalilin daukar wannan mataki ba.
Sanarwar ta ce, “Da wannan mataki, an janye dukkan gata da haƙƙoƙin da suka shafi ofishinsa na mai ba da shawara na musamman ga Gwamna kan harkokin Majalisar Dokoki ta Kasa.”
Haka kuma sanarwar ta umarci tsohon mai ba da shawarar da ya gaggauta mika dukkan kadarorin gwamnati da ke hannunsa ga ofishin sakataren gwamnatin jihar.
-
News1 day ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News22 hours ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News2 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
