Connect with us

News

Ranar Jinkai ta Duniya: Gudauniyar AMG ta ba da tallafin Naira Miliyan 25 ga asusun jinkai na gwamnatin Kano

Published

on

FB IMG 1755699070474

A ya yin da a ke bikin ranar jin kai ta duniya na 2025, gudauniyar Aminu Magashi Garba (AMG) ta bayyana goyon bayanta ga kafa asusun jinkai na jihar Kano tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Harkokin Jin Kai da Rage Talauci ta jihar.

Gudauniyar ta AMG ta kuduri aniyar tallafawa shirin gudanar da taron bita na kwana ɗaya domin tattauna muhimmancin kafa wannan asusu da kuma amfaninsa.

Advertisement

Kotu Ta Hana Tsohon Shugaban NNPCL Amfani Da Asusun Bankinsa Huɗu

AMG ta ce wannan asusu na nufin ƙarfafa haɗin gwiwa da sabbin hanyoyin samar da kuɗaɗe domin ayyukan agaji na gaggawa da kuma dabarun kula da annoba idan ta faru.

 

Advertisement

Bugu da ƙari, gudauniyar ta AMG ta bayyana cewa za ta tallafa wajen matsin lamba na dokoki, ciki har da shirya kudirin doka domin kafa wannan asusu na jinkai.

Wannan ƙuduri ya yi daidai da tallafin Naira miliyan 25 da gudauniyar ta bayar a matsayin “capital receipt” na Ma’aikatar Harkokin Jin Kai da Rage Talauci a kasafin kudin shekarar 2025.

Advertisement

Za a yi amfani da kuɗaɗen wajen gina ƙwarewa, bayar da tallafin fasaha da kuma wayar da kai.

Dr. Aminu Magashi ya bayyana cewa: “A yau, bisa taken ‘Ƙarfafa Haɗin Kan Duniya da Ƙarfafa Al’ummomi na Gida’, na rungumi muradin jama’ar Kano na samun wani asusun da aka kirkira da zai magance kalubalen jin kai da dama da ake fuskanta a jihar.”

Advertisement

Ya kuma taya Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf murna bisa ɗaukar matakin kafa Ma’aikatar Harkokin Jin Kai da Rage Talauci ta jihar.

Haka zalika, ya yaba da Majalisar Dokokin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Rt. Hon. Jibril Isma’il Falgore saboda kafa kwamitin majalisa kan harkokin jin kai, wanda Hon. Sule Lawan Shuwaki ke jagoranta.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending