News
Mutane Sama Da 50 Sun Rasa Rayuka A Sabbin Hare-haren Yan Bindiga A Katsina
Aƙalla mutane 50 ne aka kashe a hare-haren da ‘yan bindiga suka kai a ƙauyukan Karamar Hukumar Malumfashi a Jihar Katsina.
Ɗan majalisar jihar mai wakiltar yankin, Hon. Aminu Ibrahim, ya shaida wa majalisar dokoki cewa an kashe mutum 30 a lokacin sallar Asuba, sannan wasu 20 kuma aka ƙone da ransu a wasu kauyuka da suka haɗa da Gidan Adamu Mantau, Unguwar Yar Mai Dabo, Makera da Burdigau.
Ya ce mazauna yankin sun kira jami’an tsaro a lokacin da hare-haren ke faruwa, amma sai sojoji suka iso daga baya suka kuma tafi ba tare da tsare yankin ba.
“Mutanenmu sun shiga halin tsoro da bakin ciki. Ba za su iya ci gaba da rayuwa a kauyukansu ba saboda waɗannan hare-hare,” in ji shi, yana roƙon kafa sansanonin sojoji a yankin.
Da safiyar Talata, an sake kai hari a Unguwar Mantau inda aka harbe mutane 30 a cikin masallaci yayin da suke sallar Asuba.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Katsina, Dr. Nasir Mu’azu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce gwamnati ta bayar da umarnin ƙara tsaro tare da kai tallafi ga waɗanda abin ya shafa.
