Connect with us

News

Kotu Ta Yanke Wa Malamin Islamiyya Daurin Shekara 21 A Gidan Gyaran Hali A Kano 

Published

on

Kotu

Wata Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 14, karkashin Mai Shari’a Maryam Sabo, ta yanke wa wani malamin Islamiyya, Nasif Shua’aibu ɗaurin shekara 21 a gidan gyaran hali da tarar Naira 200,00 bayan kama shi da laifin yi wa ɗalibarsa mai shekara 9 fyaɗe.

Lauyan mai gabatar da ƙara, Barista Fa’iza Dahiru Sidi, ta gabatar da shaidu guda biyar a gaban kotu, yayin da lauyan wanda ake ƙara Barista Aminu Umar ya gabatar da shaida guda ɗaya.

Advertisement

Amaechi Ya Caccaki Shugaba Tinubu Kan Yunwar Da Ta Addabi Ƴan Najeriya

A ƙarshe kotu ta tabbatar wa wanda ake tuhuma laifinsa, inda ta yanke hukuncin ɗaurin shekaru 14 a gidan yari kan laifin fyaɗe da kuma shekaru 7 kan laifin lalata yarinya.

Sannan kotun ta umarci wanda aka yanke wa hukuncin ya biya Naira 50,000 ga yarinyar da abin ya shafa.

Advertisement

 

 

Advertisement

AMINIYA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending