News
Ya Kamata Al, umma Su Rubbaya Kokarin Su Wajen Baiwa Makarantu Islamiyya Kulawar Ya Dace — Sarki Sunusi
DAGA AMINA ABDULLAHI MAI KANO
Maimartaba Sarkin Kano Malam Muhammad Sunusi II yayi kira ga iyaye dasu cigaba da rubbaya kokarin su wajen baiwa Makarantu islamiyya kulawar ya dace .
Malam Muhammad Sunusi II yayi bayyana a lokacin saukar Karatun Alkurani Mai girma a Makarantar Sheikh Nasiru Hamisu Islamiyya dake Rijiyar Zaki a Karamar hukumar Ungogo.
Mai Martaba ya godewa Malam makaranta da iyaye da suke baiwa bangaren ilimin.
Nyesom Wike Ya Kwace Filin Buhari, Abbas, Akume Da Wasu Mutane 756 A Abuja
Shima da yake nasa jawabin mataimakin shugaban makarantar, Muhammad Nasir Hamisu, yace Makarantar yanzu Dalibai 112 suka sauke Alkurani Mai girma a wannan.
Ansa jawabin sa Shugaban karamar Hukumar Ungogo Alhaji Tijjani Amiru Bilyamu Wanda Mataimakin sa Alhaji Auwalu Isa Idris ya ce majalisar karamar Hukumar Ungogo zata cigaba da tallafawa Makarantun Islamiyu domin samar da nagartacciyar al’umma.
Suma wasu daga cikin daliban da suka samu damar sauke al’kur’anin sun bayyana irin farin cikin da suka tsinci kansu.
Hakimin Ungogo Magajin Malam Alhaji Abdulkadir Ahmed Chedi da kansilar Mazabar Rijiyar Zaki sun godewa Malaman Makaranta da suke kulawa da Karatun yaran .
