News
’Yar Shekara 68 Ta Yi Wa Budurwa Dukan Da Ya Yi Sanadin Mutuwarta
Rundunar ’yan sandan Jihar Abia ta kama wata mata mai shekaru 68 mai suna Mrs. Victoria Madubuko, bisa zargin ta yi wa wata budurwa mai shekaru 22, Nnenna Eke, duka wanda ya yi sanadin mutuwarta.
Lamarin ya faru ne a garin Ndiambe Ozuitem da ke karamar hukumar Bende a jihar, inda rahotanni suka ce matar ta yi amfani da wani itace na gargajiya da ake kira Okpete wajen bugun budurwar bayan wata sabani da ya shiga tsakaninsu.
Gwamnatin Kano Ta Yi Gargaɗi Kan Zazzaɓi Mai Tsanani Da Ke Sa Mutum Zubar Da Jini
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Danladi Isa, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Umuahia.
A cewar kwamishinan, budurwar ta kamu da rashin lafiya sakamakon dukan da aka yi mata, inda aka garzaya da ita Asibitin Tochi, daga bisani kuma likitoci suka tabbatar da mutuwarta.
Ya ce rundunar ta fara gudanar da bincike kan lamarin, tare da tabbatar da cewa za a gurfanar da wacce ake zargin a kotu da zarar an kammala binciken.
