Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Haramta Shan Shisha

Published

on

images 2022 09 15T174033.383 701x375

Gwamnatin Kano ta sanar da haramta shan Shisha musamman wanda ya ƙunshi sanya ƙwayoyin maye a ciki kafin a shan ta, tana mai ambata dalilai na kiyaye lafiyar al’umma da tarbiyarsu.

‎Hukumar shari’a ta jihar Kano ce ta sanar da hakan biyo bayan rahotonni da ke nuna matasa na amfani da Shisha wajen shan miyagun ƙwayoyi da sauran abubuwa da suka saɓa da koyarwar addinin Musulunci.

Advertisement

Ƙungiyar ASUU Ta Fara Haɗa Kan Mambobinta Domin Fara Yajin Aiki A Najeriya

‎A cewar hukumar, wannan mataki ya zama wajibi ne bayan rahotanni da Muhasa Radio ta haɗa wanda ya fito da yadda matasa ke cakula Shisha da ƙwayoyi da sauransu.

‎“Mun fahimci matasa na amfani da Shisha wajen yin abubuwa da suka saɓa wa addini da al’ada. Wasu har suna cakuɗa ta da miyagun ƙwayoyi wanda ke illa ga jikinsu da ƙwaƙwalwarsu. Wannan ne abu da ba za mu lamunta ba,” a cewar wani babban jami’an hukumar shari’a.

Advertisement

‎Kano a baya ta haramta shan Shisha a ƙarƙashin gyaran wata doka ta hukumar yawon buɗe ido wadda tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya sanya wa hannu a shekarar 2021.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending