Labarai
Shugabar Kasar Mexico Ta Fusata Bayan Wani Namiji Ya Rungumeta Ya Yi Yunkurin Sumbatarta A Bainar Jama’a

Shugabar Mexico, Claudia Sheinbaum, ta yi Allah-wadai da wani lamarin cin zarafi da ta fuskanta, bayan da wani mutum ya rungumeta daga baya tare da kokarin sumbatarta a wuya yayin da take gaisawa da jama’a a kan titi.
Lamarin ya faru ne a birnin Mexico City, kusa da fadar shugaban kasa, yayin da shugabar take mu’amala da magoya bayanta – wani salo da ta sha yin amfani da shi tun kafin hawanta mulki.
Binciken Bbc Ya Kasa Gano Gaskiyar Bayanan Da Trump Ya Dogara Da Su Kan Kisan Kiristoci A Najeriya
Bidiyon da ya karade shafukan sada zumunta ya nuna yadda mutumin ya tunkare ta daga baya, ya rungumeta tare da yunƙurin sumbata, kafin jami’an tsaro su yi gaggawar shiga tsakani suka janye shi.
An ga shugabar na motsa baya cikin razana, yayin da aka kame mutumin nan take. A yanzu haka, yana a hannun jami’an tsaro.
