Labarai
Kotu ta daure wata Uwa da ta tallafawa dan ta ya damfari mutane ta Internet

Daga maryam bashir musa
Wata babbar kotun tarayya da ke zama a birnin Benin, ta yanke wa Debest Osarumwense, mahaifiyar wani mutum mai suna Endurance Osarumwense, bisa tallafawa da ta yi dan ta ya yi damfarar kudade a shafin internet.
Jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ne ta gurfanar da Debest a gaban kuliya, bisa tuhumar ta da laifin taimaka wa danta wajen karbar kudi Naira miliyan 91,296,150.00 na kudade.
Kotun ta kuma daure Debest Osarumwense na tsawon shekaru biyar a gidan ajiya da gyaran hali a Benin
-
Labarai6 days ago
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Yi Wa Masu Digirin Ƙasashen Waje Jarrabawa
-
Labarai2 days ago
Jami’an Tsaro A Pakistan Sun Kama ’Yan Najeriya 20 Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
-
Labarai6 days ago
An Kashe Mutane 418, An Yi Garkuwa Da 227 Cikin Watanni Biyu A Nijeriya — Rundunar Ƴansanda
