News
Dangote Ya Janye Ƙarar Da Ya Shigar Da Tsohon Shugaban Hukumar NMDPRA A ICPC
Lauyan Aliko Dangote, Dakta O.J. Onoja, SAN, ya rubuta wa Hukumar Kula da Ayyukan Cin Hanci da Rashawa Mai Zaman Kanta (ICPC) wasiƙa, inda ya nemi a janye karar da mai gidansa ya shigar da Injiniya Farouk Ahmed, tsohon shugaban hukumar NMDPRA.
Wasikar da aka rubuta wa ICPC mai kwanan wata 5 ga Janairu, 2025, mai taken “Sanarwar Janye Karar Da Aka Shigar Kan Injiniya Farouk Ahmed,” ta bayyana cewa, wata hukumar gwamnati da ba a ambaci sunanta ba ta karɓi ragamar binciken.
Shekaru Hudu Da Rasuwar Fitaccen Malamin Hadisi, Sheikh Dr. Ahmad Ibrahim Bamba
Da yake mayar da martani kan wannan wasika, kakakin ICPC, John Odey, ya bayyana cewa, duk da bukatar janye karar amma za a ci gaba da bincike domin ICPC na aiki ne don kare martabar kasa daga masu zagon kasa ga tattalin arzikin kasa.
