Connect with us

News

Jami’an Yansanda  Sun Cafke Wani Mahaifi Bisa Zargin Cin Zarafin Ƴarsa Mai Shekara 8 A Bauchi

Published

on

Yan sanda sun cafke wani ango a ranar ɗaurin aurensa kan zargin kisan kai

Rundunar ƴansandan jihar Bauchi ta cafke wani magidanci, mai shekaru 28, bisa zargin aikata lalata da ’yar cikinsa mai shekara takwas, inda ake zarginsa da yi mata fyaɗe ta gabanta da bayanta.

Wani ɗan uwa ga wanda ake zargin ne ya kai rahoton lamarin a ranar 31 ga Disambar 2025 a babban ofishin ƴansanda da ke Alƙaleri. A cewar rahoton, lamarin ya faru ne a ranar 30 ga Disambar 2025, sai dai rundunar ta ce ta sakaye sunan yarinyar domin kare mutuncinta.

Advertisement

Amurka Ta Kama Tsohon Ministan Kudin Ghana, Ken Ofori-Atta

Kakakin ƴansandan jihar Bauchi, SP Nafiu Habib, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a ranar Alhamis. Ya ce, bayan samun rahoton, rundunar ta tura jami’ai ƙarƙashin jagorancin Babban Sufurintanda Kadiri Danjuma zuwa wurin da abin ya faru, inda aka kama wanda ake zargi.

SP Habib ya ƙara da cewa an garzaya da yarinyar zuwa babban asibitin Alƙaleri domin duba lafiyarta, yayin da ake ci gaba da tsare wanda ake zargi. Ya ce a yayin tuhumarsa, wanda ake zargin ya amsa laifinsa.

Advertisement

A halin yanzu, Kwamishinan ƴansandan jihar Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, ya bayar da umarni ga sashin binciken manyan laifuka da ya gudanar da cikakken bincike tare da tattara ƙwararan hujjoji kafin gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu. Rundunar ta jaddada ƙudirinta na kare haƙƙin yara da tabbatar da adalci ga duk wanda aka zalunta

 

Advertisement

 

LEADSHIP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending