Connect with us

News

Mutane Biyu Sun Rasa Rayukansu Sakamakon Faɗawa Rijiya A Kano

Published

on

1767913940452

Hukumar kashe gobara ta tabbatar da ceto gawar mutane biyu da suka faɗa cikin rijiyoyi a wasu yankuna daban-daban na jihar Kano.

Kakakin hukumar, Saminu Yusuf Abdullahi, ya shaida wa manema labarai cewa sun samu kiran gaggawa daga garin Kwankwaso da ke ƙaramar hukumar Madobi, inda wani yaro ɗan shekara biyu ya faɗa cikin rijiya.

Advertisement

Jami’an Yansanda  Sun Cafke Wani Mahaifi Bisa Zargin Cin Zarafin Ƴarsa Mai Shekara 8 A Bauchi

A wani lamari daban, ya ce jami’an hukumar sun kuma ceto gawar wani matashi mai shekaru 28 da ya faɗa rijiya a garin Kurofawa Yan Kifi da ke ƙaramar hukumar Gwarzo.

Saminu Yusuf Abdullahi ya tabbatar da cewa dukkan mutanen biyu sun rasu kafin a samu damar ceto su, duk da gaggawar da jami’an hukumar suka yi wajen kai ɗauki.

Advertisement

Ya ƙara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin faɗuwar tasu, tare da wayar da kan al’umma kan muhimmancin rufe rijiyoyi da kuma kiyaye lafiyar yara da manya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending