News
Kotu Ta Soke Belin Wanda Ake Zargi Da Lakadawa Wata Mata Duka A Kano
Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano ta sanar da samun nasarar soke belin da aka bai wa Kabiru Aminu, wanda ake tuhuma da aikata laifin duka a unguwar Danladi Nasidi da ke Karamar Hukumar Kumbotso.
Hukuncin ya fito ne daga Babbar Kotun Jiha ta 10 da ke Kano, karkashin jagorancin Mai Shari’a Aisha Yau. Kotun ta amince da bukatar masu gabatar da kara na soke belin, bisa la’akari da tsananin laifukan da ake zargin wanda ake kara da su.
Shugaba Tinubu ya sa hannu kan sabuwar dokar zaɓe
Ana tuhumar Kabiru Aminu da shiga harabar wani ba bisa ka’ida ba, fashi da makami, tare da lakadawa Hajiya Rabi duka da kuma yankarta, lamarin da ya haddasa mata raunuka.
Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta ce za ta ci gaba da bibiyar shari’ar har zuwa karshe domin tabbatar da adalci ya tabbata.
A cikin wata sanarwa da kakakin kwamishinan shari’a, Abubakar Tijjani Ibrahim ya fitar, ya jaddada cewa gwamnati na da kudurin tabbatar da bin doka da oda, tare da hukunta duk wanda aka samu da laifi.
-
Opinion4 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
