Connect with us

News

Trump ya ce Amurka na buƙatar komawa Afghanistan

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

Donald Trump ya ce yana ganin Amurka na bukatar komawa kasar Afganistan domin kwato Amurkawa da biliyoyin daloli na kayan soji.

“Yan Taliban sun tsare Amurkawa da dama. Bai kamata gwamnati ta samu wani abu ba na miƙawa Taliban dala biliyan 85. Watakila ya kamata mu koma Afganistan,” in ji tsohon shugaban a wani gangamin yakin neman zabe a Michigan.

Ya ce “wauta ne” cewa “kayan aikin soji mafi fa’ida a duniya, da suka ƙunshi manyan bindigogi 700,000” su kasance a hannun Taliban.

Mista Trump ya sha caccakar Biden na ficewa Afghanistan, yana mai kiran matakin wanda “bai dace ba.”

Advertisement

Biden ya ce gwamnatin Trump ce ta fara ɗaukar matakin wanda aka samu tsaiku na tsawon wata uku.

Tsohon shugaban ya ce gwamnatin Biden ta “ƙunyata” Amurka na ficewa Afghanistan tare da ganin lafinsa kan abin da ke faruwa a Ukraine.

Trump ya ce ya yi imanin inda shi ne shugaban ƙasa, Rasha ba za ta abka wa Ukraine ba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending