Connect with us

News

Jami’an Ƴansanda Sun Kama ‘Yan Ta’adda Da Ke Amfani Da Coci A Matsayin Maɓoya

Published

on

Rundunar ’yan sandan Jihar Akwa Ibom, ta cafke wasu ’yan ta’adda, maza da mata, waɗanda suke amfani da wata coci a matsayin maɓoyarsu.

Kakakin rundunar, DSP Timfon John, ta ce wani samame da rundunar ta kai maɓoyar ne ya kai ga nasarar kama mutane bakwai, maza huɗu da mata uku.

Advertisement

Hare-haren Ƴanbindiga Sun Yi Ajalin Mutane Aƙalla 60 A Jihohin Neja Da Kebbi

Timfon, ta bayyana cewa sun gano muggan makamai da suka haɗa da adduna, harsasai, da bindigogi.

Advertisement

Sannnan sun samu kakin ’yan sanda, babura huɗu, da wayoyin hannu 10.

Sauran abubuwan da aka gano sun haɗa da sifana, lambobin mota, da kuma wani hoto da ke da alaƙa da wani binciken sirri da rundunar ke gudanarwa.

Advertisement

“Mun samu bayanan sirri kan yadda wasu ɓata-gari ke aikata muggan laifuka a wani gida da suka yi basaja da shi a matsayin coci. Nan da nan muka tura tawaga ta musamman zuwa wajen.

“Binciken da muka gudanar ya nuna yadda waɗanda ake zargin ke amfani da addini suna aikata miyagun laifuka. Don haka, Kwamishinan ’yan sanda, CP Waheed Ayilara, ya bayar da umarnin tsananta bincike kan lamarin domin kamo babban waɗanda ake zargi,” in ji ta.

Advertisement

 

AMINIYA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending