Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Ta Karɓi ‘Yan Gudun Hijira 179 Da Suka Dawo Daga Libya

Published

on

4e711d0adb7a27cc7cbfd332eff185da6a03b0acc1bc6321edb9903642aaeaf2 MAIN 1

Gwamnatin Tarayyar Najeriya, ta hannun Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), tare da haɗin gwiwar Hukumar Kula da ‘Yan Ci-rani ta Duniya (IOM), sun karɓi wasu ‘yan Nijeriya 179 da suka dawo daga ƙasar Libya, a wani shiri na tallafa wa waɗanda ke son komawa gida da radin kansu.

A wata sanarwa da NEMA ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Laraba, ta bayyana cewa an tarbi waɗannan ‘yan ƙasar ne bayan sun iso Filin Jiragen Sama na Murtala Muhammed da ke Legas, da misalin ƙarfe 4:15 na yammacin ranar Talata, cikin jirgin Al Buraq Airlines.

Advertisement

Hare-haren Ƴanbindiga Sun Yi Ajalin Mutane Aƙalla 60 A Jihohin Neja Da Kebbi

Sanarwar ta ƙara da cewa, daga cikin waɗanda suka dawo akwai manya 162, waɗanda suka haɗa da maza 95 da mata 67. Haka kuma akwai ƙananan yara 9 da jarirai 8 da suka kasance cikin jerin masu dawowa.

Advertisement

NEMA ta ce bayan isowarsu, jami’an Hukumar Shige da Fice ta Najeriya sun gudanar da rajista tare da tattara muhimman bayanai domin tantance su da kuma sauƙaƙa yadda za a sake haɗa su da al’ummominsu.

Bugu da ƙari, an bai wa waɗanda suka dawo tallafin jinƙai, wanda ya haɗa da abinci, ruwan sha, kulawar lafiya daga jami’an kiwon lafiya, da kuma taimakon jigilar kayayyakinsu, domin tabbatar da dawowarsu cikin aminci, mutunci da kulawa.

Advertisement

Sanarwar ta kuma bayyana cewa an bai wa mutanen shawarwari na musamman, domin taimaka musu wajen sake tsayawa da ƙafafunsu da kuma haɗewa da al’umma cikin sauƙi.

Wannan na daga cikin ci gaba da ƙoƙarin da gwamnatin tarayya ke yi na dawo da ‘yan Nijeriya da suka maƙale a ƙasashen waje, musamman waɗanda ke fuskantar ƙalubale a ƙasashen Arewacin Afirka.

Advertisement

 

TRT AFRIKA 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending