Connect with us

News

Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Umarci A Kawo Sheikh Abduljabbar Domin Ya Kare Kansa A Kano

Published

on

IMG 20260327 WA0003

Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Kano ta ba da umarni ga Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta ƙasa da ta gabatar da Sheikh Abduljabbar Kabara a gabanta, domin ci gaba da sauraron ƙarar da ya ɗaukaka.

Sheikh Abduljabbar, wanda malamin addinin Musulunci ne, yana tsare ne bayan wata ƙaramar kotun shari’a ta same shi da laifin batanci tare da yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Advertisement

Makafi 135 Ne Suka Rubuta Jarrabawar JAMB A Kano

A zaman kotun da aka gudanar a ranar Litinin, jagoran alkalai, Mai shari’a Mohammed Lawal-Shuaibu, ya bayyana cewa kasancewar wanda ya shigar da ƙarar ya yi hakan da kansa ba tare da lauya ba, wajibi ne ya bayyana a gaban kotu domin kare kansa da hujjojinsa.

Advertisement

Sauran alkalan da suka zauna tare da shi sun haɗa da Mai shari’a Abubakar Mu’azu-Lamido da Mai shari’a Ahmad Ramat-Mohammed.

Alkalin ya ce dole ne a gabatar da wanda ake ƙara a gaban kotu, musamman ma kasancewar yana tsare, inda ya umurci hukumomin gidan yari da su kawo shi a ranar 23 ga Afrilu, 2026 domin ci gaba da sauraron ƙarar.

Advertisement

Kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 23 ga Afrilu, bayan da babu wani ɓangare ko wakilinsa da ya halarta a lokacin da aka fara kiran shari’ar.

A yayin zaman, wani mutum mai suna Usman Malam-Hussaini ya sanar da kotu cewa Sheikh Abduljabbar ya aiko shi da wasiƙa, yana neman a mayar da shi Kano daga gidan yarin Kuje domin samun damar duba takardunsa cikin sauƙi.

Advertisement

Daga bisani, kotun ta gayyaci Babban Lauyan Jihar Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru-Maude (SAN), da ya bayyana a gabanta, kafin ta ɗage sauraron shari’ar na ɗan lokaci.

Sai dai bayan sake kiran shari’ar, Mataimakin Daraktan Gurfanar da Ƙara na Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano, Barista Zahradeen Kofar-Mata, ya bayyana cewa Babban Lauyan jihar ba ya cikin koshin lafiya, tare da miƙa uzurinsa ga kotu.

Advertisement

Ya kuma bayyana cewa an damƙa shari’ar ga wani lauya mai zaman kansa, yana mai danganta jinkirin da aka samu da wata matsala a sashen rajista.

Sai dai kotun ta nuna rashin jin daɗinta kan rashin halartar Babban Lauyan jihar, tana mai cewa hakan na iya zama rashin girmama kotu, kafin daga bisani ta ɗage shari’ar zuwa ranar da aka tsara domin ci gaba da sauraro.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending