News
JAMB Ta Fitar Da Sakamakon jarabawar UTME Na Ranar Litinin
Hukumar Gudanar da Jarrabawar Shiga Makarantun Gaba da Sakandire (JAMB), ta fitar da sakamakon ɗaliban da suka rubuta jarabawar Unified UTME a ranar Litinin, 20 ga Afrilu, 2026.
Kakakin hukumar, Fabian Benjamin, ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka fitar a ranar Talata, inda ya umurci ɗaliban da abin ya shafa da su bi hanyoyin da aka saba amfani da su wajen duba sakamakon jarabawarsu.
Wata Mahaifiya Ta Mutu A Wajen Da ‘Yarta Ke Rubuta Jarrabawar JAMB
“An fitar da sakamakon na ranar Litinin, 20 ga wata. Ɗalibai za su iya duba sakamakonsu ta hanyar da aka saba,” in ji sanarwar.
Ana iya duba sakamakon ta hanyar aika saƙon “UTMERESULT” zuwa lambobin 55019 ko 66019 ta SMS, ta amfani da lambar waya da aka yi rajista da ita lokacin yin jarabawar.
