Connect with us

News

Matsalar Rashin Ruwa Na Cigaba Da Tsananta A Wasu Sassan Jihar Kano

Published

on

1713621381072

Matsalar rashin wadataccen ruwan sha na ci gaba da tsananta a wasu sassan Jihar Kano, musamman a wannan lokaci na tsananin zafi, lamarin da ke jefa al’umma cikin mawuyacin hali.

‎Wani bincike da jaridar Inda Ranka ta gudanar ya nuna cewa jama’a da dama a cikin birnin Kano da kewaye na fama da matsalar karancin ruwa mai tsafta, duk da alkawuran gwamnati na inganta samar da ruwa a jihar.

Advertisement

Dangote Na Shirin Gina Babbar Matatar Mai A Gabashin Afirka Don Ƙarfafa Samar Da Makamashi

‎Rahoton ya bayyana cewa mazauna wasu unguwanni na daukar lokaci mai tsawo suna neman ruwa domin bukatun yau da kullum kamar girki, wanke-wanke da kuma shan ruwa, abin da ke kara tsananta rayuwa a lokacin zafi.

Advertisement

‎Wasu daga cikin mazauna yankunan sun shaida cewa a wasu lokuta sukan kwashe sa’o’i suna jiran ruwa ko kuma neman inda za su samu, lamarin da ke janyo tsaiko a harkokin yau da kullum.

‎A lokacin yakin neman zabe da kuma bayan hawansa mulki, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi alkawarin kawo karshen matsalar ruwan sha tare da gyara ayyukan kamfanin ruwa na jihar.

Advertisement

‎Sai dai, kusan shekaru uku bayan hawansa mulki, wasu mazauna na cewa har yanzu ba su ga wani gagarumin sauyi ba, yayin da a wasu yankuna ake ganin matsalar ta kara tsananta.

‎Binciken ya kuma nuna cewa a wasu unguwanni, tankunan motocin daukar ruwa sun zama wata muhimmiyar hanya ta samar da ruwa, inda ake sayar wa jama’a a jarkoki.

Advertisement

‎Hakan na kara jefa iyalai cikin tsadar rayuwa, musamman ganin yadda bukatar ruwa ke karuwa a lokacin zafi.

‎Wasu mazauna sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta dauki matakan gaggawa domin magance matsalar, tare da tabbatar da samar da wadataccen ruwan sha ga al’umma.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending