News
Jami’an ‘Yansanda Sun Kama Mutane 4 Da Ake Zargi Da Fashi Da Makami A Kaduna
Rundunar ‘yan sanda ta sanar da kama wasu mutane hudu da ake zargi da hannu a ayyukan fashi da makami a Jihar Kaduna, tare da kwato makamai da alburusai a wani samame da aka kai bisa bayanan sirri.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce jami’an Sashen Leken Asiri na Musamman (FID-STS) ne suka gudanar da samamen a ranar 7 ga Maris, 2026, a yankin Tayu da ke karamar hukumar Sanga, inda suka cafke Abdumumini Abubakar mai shekaru 40, Maikano Gambo mai shekaru 47, Saleh Thompson mai shekaru 47, da Oyonyi Odango mai shekaru 40.
Yanbindiga Sun Kai Hai Wani Gidan Marayu A Kogi
‘Yan sandan sun bayyana cewa an kama mutanen ne bayan samun sahihan bayanai da ke danganta su da ayyukan ‘yan bindiga da sauran laifuka masu nasaba da tashin hankali a yankin.
Sanarwar ta ce kayayyakin da aka kwato daga hannunsu sun hada da bindigogi kirar AK-47 guda hudu tare da alburusai guda 80 na nau’in 7.62 x 39mm, da kuma wata bindiga kirar gida mai dauke da harsasai 20 na nau’in 9mm.
A cewar rundunar, binciken farko ya nuna cewa wadanda ake zargin na daga cikin wata kungiyar masu aikata laifuka da ke aiki a yankin, inda ake ci gaba da farautar sauran mambobin da suka tsere, tare da kokarin kwato karin makamai.
