News
Rotimi Amaechi ya shiga tseren takarar shugaban ƙasa a 2023
Daga Yasir sani abdullahi
Ministan Sufuri na Ƙasa, Rotimi Amaechi ya baiyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023.
Amaechi ya baiyana cewa zai tsaya takarar ne a yau Asabar a wani taron APC a Jihar Rivers.
Ministan ya ce zai tsaya takara a zaɓen shugaban ƙasa domin ya gaji Muhammadu Buhari.
“Na tsaya a gaban ku domin na sanar muku da aniya ta ta zama shugaban kasar ku a 2023,” in ji shi.
Advertisements
