News
Iran Ta Kunyata Amurka A Idon Duniya A Wannan Yakin Da Suke Yi —Shugaban Gwamnatin Jamus
Shugaban Gwamnatin Jamus, Friedrich Merz, ya bayyana cewa bai ga wata takamaimiyar dabara da Amurka ta riƙe ba domin fitar da kanta daga yaƙin da take yi da Iran ba.
Merz ya ce, a halin yanzu, kamar yadda yake gani, shugabannin Iran na ci gaba da kunyata Amurka, yana mai cewa “ƙasar [Amurka] gaba ɗaya na fuskantar wulaƙanci daga shugabannin Iran.”
Shin Da Gaske Gwamnatin Shugaba Tinubu Za Ta Fara Karbar Harajin Siya Da Saka Sola?
Da yake tattaunawa da ɗalibai a jihar North Rhine-Westphalia, ya bayyana cewa Amurka ba ta da wata sahihiyar hanya da za ta kawo ƙarshen wannan rikici cikin gaggawa.
Ya ƙara da cewa, Iran na gudanar da tattaunawar cikin hikima da dabara, kuma ƙarfin da take da shi ya fi yadda aka yi zato a baya.
Merz ya jaddada cewa rashin tsayayyen tsari daga ɓangaren Amurka na daga cikin dalilan da suka sa har yanzu ba a ga alamar kawo ƙarshen rikicin ba, duk da ƙoƙarin da ake yi na sasanta al’amura ta hanyar diflomasiyya.
-
News1 day ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
