Connect with us

News

Gwamnatin Kano Zata Kashe Sama Da Biliyan 61 Wajen Samar Da Ayyukan Raya Kasa ‎ ‎

Published

on

fb img 1777554958186 1260x7109049681884036636187 1

Majalisar Zartarwa ta jihar Kano ta amince da kashe sama da Naira biliyan 61 domin aiwatar da ayyuka daban-daban da suka shafi ci gaban al’umma a fannoni da dama.

‎Sanarwar ta fito ne bayan zaman majalisar karo na 39 da aka gudanar a ranar Talata, 28 ga Afrilu, 2026, a Fadar Gwamnatin da ke Kano.

Advertisement

Maciji Ya Shiga Wandon Bature ‎

‎Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana wa manema labarai cewa an amince da jimillar Naira ₦61,630,882,501.98 domin ayyukan da suka shafi ilimi, lafiya, gine-gine, noma, muhalli da sauran bangarori.

Advertisement

‎Haka kuma a bangaren lafiya, an warea kudu domin gyaran asibitoci, yaki da cututtuka kamar shan inna, da samar da kayan kiwon lafiya ga mata da kananan yara.

‎A fannin ayyuka da ababen more rayuwa, majalisar ta amince da sake gina hanyoyi da dama ciki har da hanyar Panshekara zuwa Madobi, da kuma gyaran wasu muhimman gine-ginen gwamnati.

Advertisement

‎Bangaren noma ya samu kulawa ta musamman, inda aka amince da sayen taki mai yawa da kuma inganta ayyukan ban ruwa da cibiyoyin noma.

‎Haka zalika, a bangaren muhalli da albarkatun ruwa, gwamnatin ta amince da ayyukan kawata muhalli, gina rijiyoyin burtsatse, da kuma gyaran matatar ruwa ta Tamburawa.

Advertisement

‎A fannin tsare-tsaren birane kuwa, an amince da ayyukan sabunta birane, sanya sunayen tituna da lambobin gidaje, da kuma biyan diyya ga wasu ayyukan gine-gine.

‎A karshe, gwamnatin jihar ta ce wadannan shirye-shirye na daga cikin kokarinta na inganta rayuwar al’umma da bunkasa tattalin arzikin Kano, tare da alkawarin aiwatar da su cikin gaskiya da rikon amana.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending