Connect with us

News

Kamfanonin Bada Bashi Ne Suka Cire N1.5bn Daga Albashin Ma’aikatan Kano — SSG

Published

on

images (7)

Sakataren Gwamnatin Jihar Kano (SSG), Alhaji Umar Faruk Ibrahim, ya ce bincike ya tabbatar da cewa kamfanonin bada bashi ne suka cire sama da Naira biliyan 1.5 daga albashin ma’aikatan jihar, ba tare da hannun jami’an gwamnati ba.

SSG ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin bikin ranar ma’aikata ta duniya da ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC suka shirya a Fadar Gwamnatin Kano.

Advertisement

Ya ce binciken da wani kwamitin gwamnati ya gudanar tare da haɗin gwiwar wani kamfanin bincike mai zaman kansa ya gano cewa kamfanonin bada bashin ne suka yi kuskure wajen cire kuɗaɗe fiye da yadda ya dace daga albashin ma’aikatan.

A cewarsa, “Rahoton binciken ya tabbatar da cewa babu wani jami’in gwamnati da ke da hannu a lamarin. Kamfanonin bada bashi ne suka wuce gona da iri wajen cire kuɗaɗe.”

Advertisement

SSG ɗin ya ƙara da cewa an riga an cimma matsaya da kamfanonin da abin ya shafa, inda suka amince da mayar da kuɗaɗen da aka cire fiye da kima ga ma’aikatan.

Ya kuma jaddada ƙudirin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na tabbatar da kare haƙƙin ma’aikata, musamman a fannin albashi da jin daɗinsu.

Advertisement

Tun da farko, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan zargin karkatar da sama da Naira biliyan 1.5 daga albashin ma’aikata, zargin da ya samo asali tun a lokacin tsohon Shugaban Ma’aikatan Jihar, Abdullahi Musa.

Gwamnan ya bayar da wannan umarni ne a yayin bikin ranar ma’aikata ta shekarar 2026, bayan da shugaban NLC na jihar, Kabiru Inuwa, ya gabatar da ƙorafi kan lamarin.

Advertisement

Ya kuma yi alƙawarin cewa duk wanda bincike ya kama da laifi zai fuskanci hukunci tare da mayar da kuɗaɗen.

Sai dai sabon bayani daga SSG ya nuna cewa alhakin lamarin ya rataya ne a kan kamfanonin bada bashi, ba tsohon Shugaban Ma’aikatan Jihar ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending