Connect with us

Labarai

Yan bindiga sun kashe mutane fiye da 130 a Jihar Filato

Published

on

Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Daga Khadija abdullahi muhmd

 

 

 

Bayanan da ke fitowa daga Jihar Filato na nuni da cewa an kashe mutum 135 yayin wasu hare-hare da ‘yan bindiga suka kai a wasu ƙauyuka ranar Lahadi.

Maharan sun far wa a aƙalla ƙauyuka hudu da ke Ƙaramar Hukumar Kanam a kan babura, inda suka dinga harbe mutane tare da ƙona gidaje masu ɗumbin yawa da kuma sace shanu.

Advertisement

Hukumomi ba su yi cikakken bayuani game da hare-haren ba.

Sai dai wani basaraken gargajiya a yankin yace tuni aka gano gawar mutum 54 a kauyen Kukawa da kuma gawar mutum 34 a kauyen Gyambau

Ya kara da cewa an kashe mutum talatin da daya a wasu kauyuka biyu.

Kana an kashe ‘yan kato-da-gora akalla 16 a kauyen Shuwaka.

Bayanai sun nuna cewa cikin wadanda aka kashe har da kananan yara da matasa.

Mutane da dama ne suka ɓace sakamakon harin yayin da lamarin ya raba daruruwan mutane daga muhallansu.

Advertisement

Mazauna yankin sun yi zargin cewa an kwasshe kusan kwana guda kafin jami’an tsarto su kai musu dauki.

Sun kara da cewa wadannan su ne hare-hare mafiya muni da aka taba kai wa a yankin.

Hukumomi sun ce an tura ƙarin jami’an tsaro a yankin.

Jihar Filato ta sha fama da rikicie-rikice da ke da nasaba da ƙabilanci da kuma addini, amma a baya-bayan nan ‘yan fashin daji da masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa sun ta’azzara matsalar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending