News
Yanzu-yanzu: Sanata Adamu da Sanata Kyari sun yi murabus daga majalisar dattawa
Daga kabiru basiru fulatan
Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Abdullahi Adamu, ya yi murabus daga majalisar dattawar tarayya.
An zabi Abdullahi Adamu ne matsayin sabon shugaban jam’iyyar APC a ranar 26 ga Maris yayin taron gangamin jam’iyyar.
Ya shiga majalisa tun shekarar 2011 har ila yau da yayi murabus.
Hakazalika mataimakin shugaban jam’iyyar APC mai wakiltan Arewa, Sanata Abubakar Kyari, ya yi murabus.
Gabanin murabus dinsa, Sanata Kyari ya wakilci mazabar Borno ta Arewa.
Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya sanar da hakan a wasikun da ya karanta ranar Talata.
Birnin tarayya Abuja – Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Abdullahi Adamu, ya yi murabus daga majalisar dattawar tarayya.