News
Gwamnatin Kano Ta Ayyana Talata A Matsayin Ranar Hutun Sabuwar Shekarar Musulunci Ta 1448AH
Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana ranar Talata, 16 ga Yunin 2026, a matsayin ranar hutu a fadin jihar domin bai wa al’ummar Musulmi damar gudanar da bukukuwan shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1448 Hijiriyya.
Sanarwar ta fito ne daga Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, a madadin gwamnatin jihar.
Gwamnatin Kano Ta Ayyana Talata A Matsayin Ranar Hutun Murnar Sabuwar Shekarar Musulunci Ta 1448AH
A sakon taya murna da ya aikewa al’ummar Musulmi, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana farin cikinsa bisa samun damar shaida sabuwar shekarar Musulunci, wadda ta fara da watan Muharram, watan farko a kalandar Musulunci.
Gwamnan ya yi kira ga al’ummar jihar da daukacin Musulmi da su yi nazari a kan ayyukansu da mu’amalolinsu na shekarar da ta gabata, tare da amfani da wannan lokaci wajen neman gafarar Allah da yin addu’o’in samun zaman lafiya, hadin kai da ci gaba ga Jihar Kano da Najeriya baki daya.
Ya kuma tabbatar wa al’ummar jihar cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da suka shafi walwalar jama’a da inganta rayuwarsu, ta hanyar samar da shugabanci nagari da ke mayar da hankali kan bukatun al’umma.
Gwamna Yusuf ya yi addu’ar Allah Ya sanya sabuwar shekarar Musuluncin ta kasance mai cike da albarka, zaman lafiya da ci gaba ga al’ummar Kano da kasa baki daya.
Sanarwar ta bukaci mazauna jihar da su yi amfani da wannan lokaci wajen karfafa zumunci, hadin kai da zaman lafiya a tsakanin al’umma.
