News
Rikici Kan Bashin Naira 500 Ya Jawo Mutuwar Tsoho Mai Shekara 65
Wani tsoho mai shekaru 65 ya rasa ransa a Jihar Ondo bayan wata takaddama da ta samo asali daga bashin naira 500 da ake zargin ya bai wa dansa na riko.
Lamarin ya faru ne a garin Oda da ke Karamar Hukumar Akure ta Kudu, inda rahotanni suka ce takaddamar da ta fara da neman a biya bashin ta rikide zuwa fada, lamarin da ya kai ga mutuwar tsohon.
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
Majiyoyi sun bayyana cewa mamacin ya bukaci dansa na riko, Kingsley Nsikak, da ya mayar masa da naira 500 da ake zargin ya karba daga hannunsa. Sai dai bukatar ta haifar da cacar baki tsakanin su, wadda daga bisani ta rikide zuwa artabu.
Shaidu sun ce tsohon ya samu munanan raunuka yayin rikicin, inda aka garzaya da shi asibiti domin ceto rayuwarsa. Sai dai an tabbatar da rasuwarsa yayin da yake karbar kulawar likitoci.
Wani dan uwan mamacin, James Ugolo, ya ce rikicin ya auku ne bayan bangarorin biyu sun sha barasa. A cewarsa, yayin da ake fadan ne tsohon ya fadi tare da bugun kansa a wani abu mai karfi, abin da ya haddasa raunukan da suka kai ga mutuwarsa.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ondo ta tabbatar da kama Kingsley Nsikak bisa zargin hannu a lamarin. Kakakin rundunar ya ce an mika binciken zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID) domin zurfafa bincike kan abin da ya faru.
Ya kara da cewa wanda ake zargin na tsare a hannun ’yan sanda, kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala bincike.
