Connect with us

News

Gwamnatin Oyo Ta Sanya Dokar Hana Fita A Kananan Hukumomi 10 Saboda Matsalar Tsaro

Published

on

Oyo State Governor Seyi Makinde 1 (1)

Gwamnatin Jihar Oyo ta ayyana dokar hana fita ta sa’o’i 16 a kananan hukumomi 10 da ke makwabtaka da Tsohon Dajin Oyo National Park, a wani yunkuri na ƙarfafa matakan tsaro da daƙile duk wani barazana ga zaman lafiya a yankunan.

Wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Musibau Babatunde, ya fitar ta ce Gwamna Seyi Makinde ya amince da sanya dokar, wadda za ta fara aiki daga ranar Laraba, 24 ga Yunin 2026.

Advertisement

Bayan Kwana 126 A Tsare Kotu Ta Sake Dage Shari’ar El-rufai Zuwa Watan Satumba

A cewar sanarwar, dokar hana fitar za ta rika aiki daga ƙarfe 4:00 na yamma zuwa ƙarfe 8:00 na safe a kowace rana, kuma za a fara aiwatar da ita na tsawon sa’o’i 48 a matakin farko.

Advertisement

Kananan hukumomin da dokar ta shafa sun haɗa da Oriire, Orelope, Irepo, Saki West, Saki East, Atisbo, Itesiwaju, Iseyin, Olorunsogo da Atiba, dukkansu na daga cikin yankunan da ke kusa da Tsohon Dajin Oyo National Park.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarin da take yi na tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a yankunan da abin ya shafa.

Advertisement

Haka kuma, ta buƙaci mazauna yankunan su bi umarnin da aka gindaya tare da bai wa jami’an tsaro cikakken haɗin kai domin tabbatar da nasarar aikin wanzar da zaman lafiya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending