Connect with us

News

Ƙarancin Wutar Lantarki Ya Sa An Fara Bayar Da Hayar ‘Power Bank’ A Kano 

Published

on

We pay N300 to charge our phones 768x859 (1)
Advertisements
ads

Ƙarancin wutar lantarki a Jihar Kano ya sa wasu matasa a unguwar Kwanar Ungogo suka fara sana’ar bayar da hayar Power Bank domin sauƙaƙa wa jama’a cajin wayoyinsu.

Ana bayar da na’urar kan naira ɗari uku (300) na tsawon sa’o’i ashirin da huɗu (24).

Kwamitin CVR Na Kano Ya Haɗa Gwiwa Da Ƙungiyoyin Ƙwadago Don Ƙara Yawan Masu Rajistar Katin Zaɓe

Ɗaya daga cikin masu gudanar da sana’ar, Mahmud Sulaiman Bawa, ya ce kafin shiga harkar yana sayar da lemun kwalba, amma yanzu ya samu horo kan yadda ake amfani Power Bank.

Ya bayyana cewa duk wanda ya ɓatar da na’urar zai biya naira dubu biyar (5,000) a matsayin tara.

Rahotanni sun nuna cewa sana’ar ta samu karɓuwa a Kwanar Ungogo da kuma yankunan Dawanau da Rijiyar Lemo.

Advertisement

Masu amfani da ita sun ce tsarin ya rage musu wahalar neman wutar lantarki, tare da kare su daga haɗarin ɓatan wayoyinsu a wuraren caji.

 

 

Daily Trust 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending