Connect with us

Labarai

Mutum 1,500 sun rasa rayukansu a watan jiya sanadin tabarbarewar tsaro a Najeriya’.

Published

on

Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

 

 

Wani rahoto kan sha’anin tsaro ya ce an kashe kusan mutum 1,500 cikin watan jiya a Najeriya, sanadin ayyukan taɓarɓarewar tsaro da hare-haren ‘yan fashin daji.

Bayanin na ƙunshe ne cikin rahotonnin tsaro na wata-wata wanda wani kamfanin harkokin tsaro mai suna Beacon Consulting yake wallafawa

A cewarsa, ƙoƙarin gwamnati na hana ƙaruwar hare-hare da kashe-kashe da satar mutane don neman kuɗin fansa ya gaza a watan Maris, inda aka sace mutum 702.

Advertisement

Rahoton ya ce sakamakon tabarbarewar tsaro a kasar ta Najeriya musaman a yankin arewa maso yammacin kasar an samu mace macen mutum 1,497.

Rahoton ya ce alkaluman da aka samu nada nasaba da yadda mahara suka fara amfani da bama bamai wanda ake sarrafawa a gida wanda ake kira IED.

Shugaban kamfanin na Beacon wanda kwarare ne kan harkar tsaro Dr Kabiru Adamu ya shaidawa BBC cewa abubuwa da dama ne suka janyo taɓarɓarewar tsaron.

“Abubuwa da yawa ne suka janyo wadanan mace mace toh amma wanda ya fi tasiri duk a cikinsu shi ne hare haren da ‘yan bindiga ke kai wa kauyuka” in ji shi.

Rahoton ya kuma ce ‘yan bindiga na kai wa jami’an tsaro da matafiya hare haren kwantar bauna kuma a yanzu suna amfani da bama bamai tare da bude wa mazauna kauyuka wuta

Nazarin da suka yi ya nuna cewa an samu karin sace -sacen mutanen domin karbar kudin fansa da kashi 41 da digo 1 cikin 100 kuma a mace macen mutane an samu kari na kashi 68 da digo 8 cikin 100 a tsakanin watan biyu da watan uku.

Advertisement

Rahoton ya bayyana rashin ingantaccen tsaro a kauyuka a matsayin babban dalilin da ya sa aka samu karuwa.

A cewar Dr Kabiru “Tsarin da ake bi a kasa yanzu bai ba ma kauyuka muhimmanci ba saboda haka akwai gibi”

Sai dai masanin ya ce wani abu da ya basu mammaki shi ne a kaso na farko na wannan shekara na nazarin da suka yi sun ga cewa a watanni uku an samu mace mace dubu 3,586 a kasar baki daya amma a bangare bangare an samu 1,373 a arewa maso yamma, ya yin da an samu 958 a yankin arewa maso tsakiyya , a yankin arewa baki daya kuwa adadin ya karu da kashi 87 da digo 1

Rahoton na zuwa a dai dai lokacin da ‘yan fashin daji ke ci gaba da kai hare hare a yankin arewa maso yamma da jihohin da ke tsakiyar kasar,

Na baya baya nan shi ne harin a ‘yan bindiga su ka kai a wasu kauyuka a jihar Filato da ya yi sanadin mutuwar mutum sama da 150.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending