Connect with us

News

Amurka za ta sayar wa Najeriya makamai na dala biliyan daya

Published

on

Daga maryam bashir musa

 

 

 

Amurka ta amince ta sayar wa Najeriya makamai da kudinsu ya kai na dala biliyan dPaya da zummar karfafa yaki da kungiyoyi masu rike da makamai.

A wata sanarwa da hukumar hadin kai game da tsaro ta Amurka ta fitar, ta ce Najeriya ta bukaci sayen jiragen helikwafta 12 masu kai hare-hare da makami mai kai hari inda aka nufa ba tare da matsala ba.

Amurka ta ce daga yanzu Najeriya ba za ta fuskanci wata matsala ba wajen sayen makamai daga wurin ta.

Advertisement

Sai dai ana sa rai wannan batun zai dauki akalla shekaru biyar kafin a kammala shi – domin kuwa zai hada da horas da dakarun tsaron Najeriya kan yadda za su yi aiki da makaman da kuma kauce wa kai hari kan fararen-hula.

Wannan ne karo na biyu da Amurka ke sayar wa Najeriya makamai cikin shekaru biyar.

A baya gwamnatin Barack Obama ta ki sayar wa Najeriya makamai bisa zargin take hakkin dan adam.

Sai dai a shekarar 2017, gwamnatin Donald Trump ta amince ta sayar wa Najeriya jiragen yaki samfurin Super Tucano guda 12.

A shekarar da ta gabata ne aka kai jiragen Najeriya

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending