Labarai
Jama’a Sun Yi Cirko-Cirko Domin Dibar Ganimar Man Da Tankar Mai Ta Zubar

Wasu ’yan Najeriya sun yi cincirindo a ranar Asabar domin dibar Ganimar man fetur da wata tankar mai ta zubar a kan babbar hanyar Lagos-Ibadan, kusa da hanyar Ibadan zuwa Ijebu-Ode.
Mazauna yankin, ciki har da mata, sun garzaya wurin dauke da bokiti, jarkoki da sauran kwantena domin dibar man da ya malale a hanya.
Ni Ba Barawon Kuɗin Gwamnati Ba Ne, Akuya Ɗaya Ce Sanadiyyar Arzikina — Dino Melaye
Wasu daga cikinsu sun rika dibar man daga magudanan ruwa, inda man ya taru, duk da hadarin da ke tattare da hakan na iya haddasa gobara ko fashewa.
Lamarin ya jawo hankalin jami’an Hukumar Kula da Kare Haɗarin Ababen Hawa ta Tarayya (FRSC) da jami’an kashe gobara, wadanda suka isa wurin domin dakile barazanar da malalar man ke haifarwa.
Jami’an agajin gaggawa sun tsare wurin tare da kokarin hana jama’a kara matsowa kusa da inda man ya zube, saboda hadarin gobara.
Duk da kokarin jami’an tsaro da na agajin gaggawa, wasu daga cikin mazauna yankin sun ci gaba da kokarin kwashe man da ya taru a magudanan ruwa.
Lamarin ya janyo damuwa kan yadda jama’a ke jefa rayukansu cikin hadari wajen dibar man fetur da ya zube, musamman ganin yadda abu kamar wuta ko tartsatsin lantarki zai iya haddasa mummunar gobara.
