Connect with us

Labarai

KANO: Mutane 18 Sun Jikkata Yayin Da Mahaukacin Kare Ya Cije Su A Garko – NFSS

Published

on

istockphoto 147694372 612x612 1
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Hukumar Tsaron Gandun Daji ta Najeriya (NFSS), reshen Garko a Jihar Kano, ta kaddamar da aikin neman wasu karnuka biyu da ake zargin sun kamu da cuta, bayan wani kare ya ciji mutane 18 a yankin.

A cewar wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na NFSS ta Jihar Kano, CSF Usman Abdullahi Umar, ya fitar, kare ya ciji mutane 11 a garin Garko kafin ya shiga wasu yankunan da ke makwabtaka da garin.

KANO: Mutane 18 Sun Jikkata Yayin Da Mahaukacin Kare Ya Cije Su A Garko – NFSS

Sanarwar ta ce daga cikin wuraren da karen ya shiga akwai Raba, Kadage, Gurjiya da Dausai, inda ya sake cizon wasu mutane bakwai, lamarin da ya kai adadin waɗanda aka ruwaito sun ji rauni zuwa 18.

Hukumar ta ce akwai wasu karnuka biyu da ake zargin sun kamu da cuta, kuma jami’anta karkashin jagorancin Jami’in Gandun Daji na sashen Garko, Auwalu Muhammad, sun fara aikin neman su domin hana sake faruwar hare-hare.

NFSS ta bukaci mazauna Garko da sauran yankunan da abin ya shafa da su kasance cikin taka-tsan-tsan tare da kai rahoton duk wani kare da ake zargin yana dauke da cutar kutta ga hukumar ko wasu jami’an tsaro.

Advertisement

Hukumar ta kuma shawarci duk wanda kare ya ciza da ya garzaya asibiti domin samun kulawar lafiya cikin gaggawa, inda ta ce jami’anta za su ci gaba da aikin neman karnukan har sai an shawo kan barazanar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending