Connect with us

Labarai

Jam’iyyar ADC Ta Buƙaci Fadar Shugaban Kasa   Ta Bayyana Wa Ƴan Najeriya Inda Shugaba Tinubu Yake

Published

on

Tinubu Bola 750x430
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar hamayya ta African Democratic Congress ADC ya buƙaci fadar shugaban ƙasar da ta fito fili ta bayyana ainihin inda Shugaba Bola Ahmed Tinubu yake.

Wannan buƙata na ƙunshe ne a wata sanarwa da ta samu sa hannun daraktan yaɗa labarai na kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar, Kola Ologbondiyan a wannan Lahadi, kwanaki 6 bayan cikar wa’adin hutun makwanni uku da shugaban ya ɗauka tun da fari, wanda ya kamata ya ƙare tun ranar 21 ga watan Satumba.

Gwamnatin Kano Za Ta Kashe Sama Da Naira Biliyan 144 Domin Ayyukan Raya Kasa

Jam’iyyar ta nuna damuwa kan yadda shugaban ya tsawaita zamansa a ƙasashen waje ba tare da wani gamsasshen bayani ga ƴan ƙasa ba.

ADC ta jaddada cewa kujerar shugaban ƙasa amana ce ta al’umma, don haka mutane fiye da miliyan 200 da suka zaɓi shugaban suna da cikakken haƙƙin sanin inda yake da kuma dalilin da ya sa bai dawo ba.

Bugu da ƙari, jam’iyyar ta soki yadda ake tafiyar da lamarin cikin sirri da kuma rahoton cewa an umurci Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, da ya cigaba da wakiltar shugaban ƙasa a tarukan gwamnati.

Advertisement

ADC ta nuna cewa wannan tsari bai amsa tambayar da ƴan ƙasa ke yi ba na wanda tsarin mulki tasahale wa jan ragamar ƙasar a irin halin da ake ciki yanzu.

 

RFI

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending