News
Rikicin Kabilanci Ya Yi Sanadiyyar Konewar Gidaje Kusan 340 A Taraba
Akalla mutane 1,000 sun rasa matsugunansu sakamakon sabon rikicin kabilanci tsakanin Mambilla da Fulani a Mbamnga, Ƙaramar Hukumar Sardauna ta Jihar Taraba.
Rikicin ya kuma yi sanadin konewar gidaje kusan 340, lamarin da ya tilasta wa wasu mazauna yankin tserewa zuwa ƙasar Kamaru da wasu garuruwan da ke makwabtaka da yankin.
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Wani Matashi Kan Zargin Hallaka Mahaifinsa Mai Shekaru 80 A Katsina
Wasu shaidu sun ce an kashe mutane da dama, ciki har da wani jami’in Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), yayin da wasu kuma ake zargin sun ɓace. Sai dai har yanzu ba a tabbatar da adadin mutanen da suka mutu ko suka ɓace ba.
Haka kuma, an kashe ko sace dabbobi, yayin da aka lalata kayan abinci da sauran hanyoyin samun abin dogaro na al’ummar yankin.
Wani mazaunin yankin, Ardo Bashiru, ya ce an shafe kusan kwanaki uku ana fadan tun daga ranar 16 ga Satumba, inda aka lalata gidaje da dama a ƙauyukan Geroji da Mbara.
Ya yi kira ga gwamnati da hukumomin agaji da su gaggauta kai wa waɗanda abin ya shafa abinci, matsuguni da sauran kayan agaji, musamman ganin yadda ake ci gaba da samun ruwan sama a yankin.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Sardauna, Alhaji Mohammed Umar, ya tabbatar da faruwar rikicin, yana mai cewa ya samo asali ne daga wata takaddama tsakanin wata mata ’yar Mambilla da wani makiyayi Bafulatani a wata gona.
Ya ce an tura jami’an tsaro yankin domin dawo da zaman lafiya, tare da ɗaukar matakan ganin an dawo da mutanen da suka tsere zuwa Kamaru.
Shi ma Sarkin Mbamnga, Alhaji Abubakar Saleh, ya yi kira ga al’ummar yankin da su kwantar da hankula tare da guje wa duk wani mataki da ka iya sake haifar da tashin hankali.
