News
Ruwan Famfo Na Daf Da Dawowa A Kano: Madalla Gwamna Abba
Daga Abba Anwar
Gagarumin aiki kan matatun ruwanmu na jihar Kano da shimfida bututu a hanyoyin ruwa da gyara matsalolin ragowar injuna dake samar da ruwan famfo mai lafiya, da Gwamna Abba Kabir Yusuf yake kammalawa, na nuni da cewar cikin ‘yan kwanaki masu zuwa kadan za a fara samun wadatar ruwan sha a Kano. Da Izinin Allah.
Hakan ke nuni da cewa ƙarni na ƙishirwa a Kano ya zo ƙarshe. Gwamna Injiniya Abba, ya mayar da tsaiko da aka yi na shekaru 95 zuwa wani sabon tarihi na zuba zunzurutun kudi har Naira Biliyan 21.3. Wannan ba magana ba ce kawai sakaka, jagoranci ne, jajircewa da kuma nuna cikakken kishin ƙasa.
Abin da ke faruwa a Kano yanzu ya cancanci duniya ta saurara. A Cape Town, sun kira ƙarancin ruwa da “Day Zero” – ranar da duniya za ta wayi gari ba ruwa. A Flint, Amurka, gubar dalma ce ta zama bala’i. Amma a Kano – birni mafi yawan jama’a a Arewacin Najeriya – abin ya zo ne a hankali, cikin shiru, amma ya fi kowanne raɗaɗi. Sama da shekaru goma, famfo ya bushe. Babu sanarwa, babu gargadi. Iska kaɗai ke fita.
LISSAFI MAI BAN TSORO
Kano na buƙatar Lita Miliyan 700 a kowace rana domin ta rayu. Har zuwa bara, tana samun ƙasa da Lita Miliyan 300. Akwai gibi na Lita Miliyan 400. Wannan ba ƙaranci ba ne, rushewar tsari ce gaba ɗaya. Mata na tashi ƙarfe 4 na dare don neman ruwa a burtsatse. Yara na ɗaukar jarka suna yawo kilomita. Masana’antu sun durƙushe. Annobar kwalara ta ɓarke a lokuta bayan lokuta.
Wasu gwamnatoci a baya duk da sun san ainihin matsalolin, amma sun fi amincewa da shafa garin magani wajen da a ke bukatar aikin tiyata. Wato zuciyar al’umma. Shine ruwan sha. Amma gwamnatin Abba ta zaɓi yin aikin tiyatar zuciya. Kuma yanzu zuciyar ta fara bugawa.
TARIHIN SHEKARU 95: RUHIN GARI
Labarin ruwan Kano bai fara jiya ba. Ya fara ne a 1927 a zamanin Sarki Abdullahi Bayero da Turawan mulkin mallaka suka kafa gidan ruwa na Challawa wanda shine na farko a Arewacin Najeriya. An kammala shi a 1930 da ƙarfin samar da Lita Miliyan 20.
Sai Tsohuwar Tamburawa a 1986 da ƙarfin Lita Miliyan 9.6, daga baya aka haɓaka zuwa Miliyan 20. Sai Sabuwar Tamburawa mai ƙarfin lita Miliyan 150. Kuma uwar duka, manyan ma’ajiyar Goron Dutse – guda biyar da aka gina tsakanin 1930 da 1974. Dan ajiye Lita sama da Miliyan 40. Su ne ruhin ruwan Kano.
Tsari ne da haziƙai suka tsara, amma sakaci da wawushewa suka kashe shi. Wannan lamari ya damu Gwamna tun kafin rantsuwarsa a 29 ga Mayu, 2023, har ya kafa Kwamitin Kwararru dan bincike da tattaro bayanai na yadda za a yi abinda ya kamata.
Da nake maganar wannan cigaba da a ka samu a Kano da wani aminina daga Darmanawa sai ya kada baki ya ce, “Wannan ƙoƙari ya cancanci goyon bayan kowa.”
Rahoton da wadancan kwararru su ka bayar ya so ya yi kama da rahoton bayanin abubuwan da suka faru a filin yaƙi. Rahoton da injiniyoyi suka ba Gwamna ya yi kama da na filin yaƙi.
A Challawa, yanayin da wajen ya fada an bayyana shi da “… mai ban tausayi da takaici”. Cikin manyan injinan samar da wuta ga injunan matatar ruwan guda shida, 2 ne kaɗai ke dingisawa. Matatar ruwa ta 1 da ta 2 sun mutu gaba ɗaya. Ta 3 tana numfasawa ne kawai da kashi 30% kacal.
Mafi muni, an yi awon gaba da kayan aiki. An sace famfon tuka ruwa, an cire na’urorin kunna wuta, an sace wayoyin ƙarƙashin ƙasa. Kuma abin da ya ba manyan Injiniyoyi mamaki, shine, an tono bututun ƙarƙashin ƙasa mai tsawon kilomita 15.6 da ke kawo ruwa Challawa an sace shi gaba ɗaya. Babu abinda ba a gani ba. Zamba baro – baro.
A Goron Dutse, labarin ya fi muni. Tafkunan da suka shayar da Kano kusan ƙarni ɗaya, sun yi shekaru goma babu digo ɗaya. Sun bushe, sun tsage, sun cika da yashi.
Jimillar ɓarnar ta haura Naira Biliyan 30. Wata gwamnati ta kashe Naira Biliyan 5.6 a watanni 11 don “kulawa” amma ba a canza bututu ba, ba a fitar da yashi ba, ba a sayi famfo ba. Sakamakon haka, Tamburawa da aka tsara ta bayar da Lita Miliyan 150 tana bayar da 27% kacal. Challawa ta Lita Miliyan 220 tana bayar da ƙasa da 30%. A tare ya kamata su bada Lita Miliyan 370, amma suna bada ƙasa da Lita Milyan 90. Domin a gyara Challawa kaɗai sai an kashe Dala Miliyan 10, saboda injinan na 1930 dole ne a ƙera su musamman a Turai.
Daukar abu da gaske ga shugaba irin yadda Gwamna Abba yake yi wato sam sam ba ya misaltuwa.
Manyan birane ba a farfaɗo da su da surutan baka kawai. Ana farfaɗo da su da himmar shugaba ta gaskiya. Anan ne Gwamna Abba ya bambanta.
Ba tura wakili yake ba, zuwa yake da kansa. Kwanan nan, shi da Mataimakinsa, H.E. Murtala Sule Garo, sanye da takalman irin na ma’aikatan ruwan, sun zagaya Challawa da Tamburawa tare da Injiniyoyin CGC Nigeria Limited da CCECC Nigeria Limited. Haka nan sun kai irin wannan ziyara ga wajen adana ruwa na Gorondutse. Shugabanci nagari.
Saboda tsananin sanin muhimmanci da ruwa yake da shi ga rayuwa da kuma addini, hakan ya sa ya amince da zuba tsabar kudade mafi girma a harkar ruwa a Kano cikin shekaru 15 da su ka gabata. Yayin da ya sa tsabar kudi har Naira Biliyan 21.29.
Ba jita-jitar Biliyan 21.89 ba. Kwangila ce da aka rattaba hannu ta Naira Bilyan 21.29. Misali Naira Biliyan 9.9 ga CGC don gyara Tamburawa. Sai Naira Biliyan 11.39 ga CCECC don gyara Challawa da farfaɗo da Goron Dutse
ME AKA YI A ƘASA?
Kamar yadda Kwamishinan Ruwa mai ci, Dr. Dahiru Muhammad Hashim ya tabbatar,
1. An maye gurbin bututun 15.6km na asbestos na 1970 da sabon bututun ƙarfe mai inganci zuwa Goron Dutse.
2. An fitar da yashi da gyara gaba ɗayan ma’ajiyun ruwa na Goron Dutse.
3. An gyara injinan tace ruwa (clarifiers), na’urorin tacewa da famfo masu matsa ruwa.
4. An sayo sabbin injunan famfo guda goma masu ƙarfin Kilowatt 110.
5. An kammala gwajin aiki a tsakiyar watan Satumba.
Haka kuma, cikin manyan famfon ruwa 19 na ƙauyuka da suka mutu, tara na kan hanyar dawowa. Guzugu a Kabo ta dawo, Joda a Gabasawa ta dawo, Wudil da ta mutu shekaru da yawa ta dawo da rai. A karon farko, karkarar Kano na cikin lissafi.
A ranar 21 ga Satumba, 2026, Ma’aikatar ta sanar da cewa za a fara raba ruwa mai tsafta nan da kwanaki ba masu jimawa ba.
DARASI DAGA DUNIYA
Daga London zuwa Legas, harkar ruwa an siyasantar da ita. Majalisar Dinkin Duniya ta ce ƙarancin ruwa zai raba mutane Miliyan 700 da muhallansu nan da 2030. Abin da Gwamna Abba ya yi darasi ne kuma babbar hobbasa ce na yadda za a juyar da akalar wannan hasashe ba tare da bashin Bankin Duniya ba, ba tare da sayar da kadarorin al’umma ba.
Bai jefa matsalar waje ba, ya biya kuɗin maganinta. Bai zargi baya ba, ya gyara gaba.
Na taba magana da Malam Musa a Tarauni yana kukan rashin ruwa. A yau da na sake tambayarsa, sai murmushi yake yi ya na cewa “Gaskiya Gwamna na iya bakin ƙoƙarinsa.”
Idan famfo a Kofar Mata ya fara tari ya ɓulɓulo, idan yaro a Dala ya sha ruwan famfo a karon farko a rayuwarsa, idan Goron Dutse ya sake cika bayan shekaru goma na fari – Kano ba ruwa kaɗai za ta yi murna ba. Za ta yi murna da Gwamnan da ya tabbatar da cewa mafarkin shekaru 95 da yashi ya binne, da bututun da aka sace, da alkawura suka gagara, na iya sake kwarara kuma a samu alfanun abin.
Wannan ba gwamnati ba ce kaɗai, daukar abu ne da dukkan muhimmanci mara jijjigewa. Daga wannan Jagora nagari.
KANO TA NA DAF DA DAWO DA RUWA ƘARƘASHIN MULKIN GWAMNA ABBA GIDA-GIDA MAI ABIN MAMAKI!
Anwar ya rubuta wannan daga Kano
Alhamis, 1 ga Watan Oktoba, 2026
