News
Babu Wani Abin Kirki A Jawabin Shugaba Tinubu Illa Kalaman Siyasa —Solomon Dalung
Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya soki jawabin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai, yana mai bayyana shi a matsayin jawabin da bai gamsar da shi ba.
Dalung ya ce jawabin, wanda Shugaba Tinubu ya gabatar a ranar 1 ga Oktoba, bai fayyace nasarorin da gwamnatin ta samu tun bayan hawanta mulki a shekarar 2023 ba, musamman ta fuskar sauye-sauyen da ta aiwatar da tasirinsu ga rayuwar ’yan Najeriya.
’Yan Bindiga Sun Hallaka Hakimin Da Suka Sace A Kano
Tsohon ministan ya bayyana cewa ya kamata Shugaban Ƙasar ya yi amfani da jawabin wajen bayyana nasarorin gwamnatinsa, tare da fayyace matakan da take ɗauka domin magance matsalolin da al’umma ke fuskanta.
Ya kuma jaddada cewa ya kamata jawabin ya tabo muhimman batutuwa da suka haɗa da matsalar tsaro, noma, tattalin arziki, rashin aikin yi, yunwa da talauci, da kuma manufofin ƙasar nan a hulɗarta da sauran ƙasashe.
Dalung ya bayyana matsayarsa ne yayin wata hira da shirin The Morning Brief na gidan talabijin na Channels Television, bayan kammala jawabin shugaban ƙasar na ranar samun ’yancin kai.
Ya ce rashin fayyace nasarorin da aka samu da kuma yadda manufofin gwamnati suka inganta rayuwar jama’a ya sa jawabin bai gamsar da shi ba.
A cewarsa, jawabin bikin samun ’yancin kai ya kamata ya zama wata dama ta yin nazari kan tafiyar gwamnati, bayyana nasarorin da aka samu da kuma gabatar da matakan magance matsalolin da har yanzu suke addabar ’yan Najeriya.
