Connect with us

News

Tsadar Rayuwa: Ma’aikatan Gwamnati Sun Fara Yajin Aikin Gargaɗi

Published

on

JNPSNC 1790868723

Kungiyoyin ma’aikatan gwamnati karkashin Majalisar Ƙasa ta Haɗin Kan Kungiyoyin Ma’aikatan Gwamnati (JNPSNC) sun umurci dukkan ma’aikatan gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi, ciki har da ma’aikatan ma’aikatu, hukumomi da sauran sassan gwamnati (MDAs), da su fara yajin aikin gargadi na kwanaki uku daga tsakar daren yau.

Kungiyoyin sun ce matakin ya biyo bayan gazawar gwamnati wajen magance bukatun da suka gabatar.

Kwankwaso Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Ci Gaba Da Marawa Sauye-Sauyen  Shugaba Tinubu Baya

Majalisar ta kuma umurci shugabannin kungiyoyin ma’aikata a matakan gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi da su tabbatar da cikakken bin umarnin yajin aikin, tana mai cewa ma’aikata da sauran ’yan Nijeriya na fuskantar ƙara taɓarɓarewar matsin tattalin arziki da na rayuwa.

An ayyana fara yajin aikin gargadin ne bayan Gwamnatin Tarayya ta gaza magance bukatun da shugabannin JNPSNC na ƙasa suka gabatar wa Shugaba Bola Tinubu cikin wata wasika mai kwanan wata 21 ga Satumba, 2026.

Majalisar ta bayyana cewa matakin ya zama dole domin matsa wa gwamnati lamba ta saurari damuwarta kan tsadar rayuwa da mawuyacin halin da ma’aikata da sauran ’yan Nijeriya masu rauni ke ciki.

Advertisement

A ranar 29 ga Satumba, majalisar ta yi barazanar fara yajin aikin gargadi na kwanaki uku idan Shugaba Tinubu bai magance bukatunta ba, ciki har da rage farashin man fetur zuwa N500 kan lita, biyan alawus ɗin albashi da daukar wasu matakai na rage radadin tsadar rayuwa.

 

 

LEADERSHIP HAUSA 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending