Connect with us

News

An Sare Wa Matashi Hannu Kan Rikicin Siyasa A Bauchi

Published

on

police arrest

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta kama mutum ɗaya, yayin da take farautar wanda ake zargin ya sare wa wani matashi hannu da wuƙa a lokacin wani rikici da ya ɓarke tsakanin matasa kan bambancin ra’ayin siyasa.

Kakakin rundunar, SP Nafi’u Habib, ne ya bayyana hakan ga manema labarai, inda ya ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 11:30 na safiyar Laraba, 14 ga Oktoba, 2026, a unguwar Bakin Kura da ke birnin Bauchi.

AWOHI Ta Raba Kayan Tallafi A Gidan Kula Da Tsofaffi Na Shahuci Dake Kano 

Ya bayyana cewa rikicin ya ɓarke ne tsakanin wani matashi mai suna Usman Idris, mai shekaru 24, da wani mutum mai suna Lawi.

A cewarsa, yayin da rikicin ke gudana, wani abokin Lawi mai suna Mamman Gore ya zo ɗauke da wuƙa mai kaifi, inda ya sare wa Usman hannu har ya faɗi ƙasa a sume.

Kakakin ’yan sandan ya ce an garzaya da wanda abin ya shafa zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, inda aka ba shi kulawar gaggawa.

Advertisement

Ya ƙara da cewa matashin na samun sauƙi a halin yanzu.

SP Habib ya ce jami’an rundunar sun kama Lawi, wanda ke taimaka wa wajen gudanar da bincike, yayin da Mamman Gore, wanda ake zargin ya sare wa matashin hannu, ya tsere.

Ya tabbatar da cewa rundunar na ci gaba da ƙoƙarin gano inda wanda ake zargin yake domin cafke shi tare da gurfanar da shi a gaban kotu.

A nasa ɓangaren, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, ya yi Allah-wadai da lamarin, yana mai gargaɗin jama’a da su guji duk wani abu da zai iya haddasa tashin hankali a jihar.

Ya jaddada cewa rundunar ba za ta lamunci duk wani yunƙuri na tayar da fitina ko kawo barazana ga zaman lafiya da tsaron al’umma ba.

Kwamishinan ya kuma yi kira ga jama’a da su riƙa warware saɓanin ra’ayoyin siyasa ta hanyar lumana, maimakon ɗaukar doka a hannu..

Advertisement

 

 

AMINIYA

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending