News
Dayyabu Auwalu matukin Adaidaita Sahu ya zama miloniya.
Dayyabu Auwalu matukin Adaidaita Sahu ya zama miloniya.
Bayan cin tarar hukumar dauka da ladabtar da yan sanda (Police Service Commission )da babbar kotun tarayya (Federal High Court)tayi, Dayyabu ya karbi cekin kudi na Naira Miliyan 3 wanda kotu tace a cira daga asusun bankin hukumar a bashi diyya sakamakon cin zarafin sa da aka yi.
Yan sandan da aka kama da laifi sun hada da Abdullahi Daura, Khalifa da kuma tsohon DPOn Kuntau Police Station Kano wato CSP Abdulhadi.
Da fatan wannan zai zama jan kunne ga yan sanda masu cin zarafin al’umma da ma ita kanta hukumar dauka da ladabtar da yan sanda din.
Alhamdulillah!
Abba Hikima
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
