Labarai
Jami’an Ƴansanda Sun Kama Mutane Takwas Bayan Rikicin Siyasar Da Ya Barke A Bichi

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta kama wasu mutane takwas da ake zargi da hannu a rikicin da ya barke tsakanin magoya bayan jam’iyyun APC da National Democratic Congress (NDC) a Karamar Hukumar Bichi ta jihar.
Rundunar ta ce mutane biyar sun jikkata, yayin da aka lalata motoci 13 a yayin rikicin da ya faru da misalin karfe 4:45 na yammacin ranar Lahadi.
Majalisar Dattawa Ta Ba Wa Jihohi Huɗu Wa’adin 17 Ga Nuwamba Kan Ƙudirin Yansandan Jihohi
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.
Sanarwar ta ce rikicin ya kuma yi sanadiyyar lalata fastoci da allunan tallata kamfen na jam’iyyun siyasar biyu.
Rundunar ta bayyana cewa jim kadan bayan samun rahoton faruwar lamarin, ta tura jami’anta zuwa yankin, inda suka yi nasarar shawo kan lamarin tare da dawo da zaman lafiya.
Ta ce kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da Gariyo guda daya, adduna biyu, sanduna masu kauri guda biyu, kwalbar wani sinadari da kuma wani abu da aka fi sani da suna ‘Suck and Die’.
