Connect with us

Siyasa

ADC Ta Kafa Kwamitin Yakin Neman Zaben Gwamna A Kano

Published

on

FB IMG 1786293088101
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Ɗan takarar gwamnan jihar Kano a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, Alhaji Ibrahim Ali Amin Little ya kafa kwamitin yaƙin neman zaɓensa, tare da naɗa Alhaji Aminu Labaran Baba a matsayin shugaban kwamitin.

Daraktan Yaɗa Labarai da Sadarwa na kwamitin, Adnan Mukhtar, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.

JIGAWA: Matashi Ya Rasa Ransa Yayin Kare Iyayensa Daga Harin ’Yan Bindiga

Sanarwar ta ce an naɗa Hon. Bala Yau Bayco a matsayin Darakta-Janar, yayin da Yusuf Mamman Bature zai riƙe muƙamin sakataren kwamitin.

Sauran waɗanda aka naɗa sun haɗa da Hon. Mamina Bako Lamido a matsayin Daraktar tuntuba, Alhaji Nasir Tahir a matsayin Daraktan Ƙungiyoyi, yayin da Adnan Mukhtar zai jagoranci ɓangaren Yaɗa Labarai da Sadarwa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending