News
YAN BINDIGA SUN KASHE MUTUM 8, SUN GINDAYA SHARADIN ZAMAN LAFIYA A JIHAR SAKKWATO.
Daga Khadija Abdullahi Mahmud.
Wasu yan bindiga a jerin gwanon Mashina sun farmaki ƙauyen Taka Lime, da ke ƙaramar hukumar Goronyo a jihar Sokoto, inda suka kashe aƙalla mutum 8.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa maharan sun tattara mutane da dama sun yi awon gaba da su, kuma sun sanar da mutanen kauyen abun da zai sa su zauna lafiya.
Wani mazaunin ƙauyen Taka Lime wanda ya rasa matarsa da ɗiyarsa a harin, Sani Takakume, ya ce yan ta’addan sun shigo kuma suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.
Ya ce:
“Mun fito da yawa ɗauke da dukkan wani nau’in makami domin mu kare kan mu daga maharan kuma muka ci nasarar kashe mutum uku, muka kama ɗaya.”
“Da suka fahimci mutanen kauye sun kashe musu mayaƙa uku, sai suka kashe mutum 8 daga cikin yan uwan mu da suke tsare da su da nufin ɗaukar fansa.”
Wane sharaɗi suka gindaya na zaman lafiya?
A cewarsa tuni yan bindigan suka bukaci a tattara musu zunzurutun kuɗi naira miliyan N10m a matsayin na fansar mutanen kauye da suka yi garkuwa da su.
Hakanan kuma sun gindaya sharaɗin cewa matukar mutane na son zaman lafiya a yankunan, dole su biya harajin miliyan N10m.
-
News3 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News5 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
