News
BAYAN GAZA BIYAN KUDIN SIYAN FAMe, ADAMU GARBA YACE YA JANYE DAGA NEMAN TAKARAR SHUGABANCIN KASA A KARKASHIN JAM´IYYAR A P C.
Daga Khadija Abdullahi Mahmud.
Adamu Garba ya ce ya fasa sayan Fam din takara kujerar shugaban kasa karkashin jam’iyyar APC
Garba ya ce kudin da jam’iyyar APC ta sanyawa Fom naira milyan dari zai halasta sata da rashawa a gwamnati
Yanzu, sun tara sama da naira milyan tamanin na gudunmuwa daga wajen mutane
A jawabin da ya saki a shafinsa ranar Talata a Abuja, Garba yace ya janye daga takarar ne saboda tsadar Fom din APC da kuma tsadar yin kamfe.
A cewarsa, sayar da Fam N100m zai maishe da siyasar Najeriya wajen cin kasuwa ne kawai ba shugabancin kwarai ba.
Daga karshe: Shugaban Majalisar Dattawa Lawan ya shiga takarar Shugaban kasa a APC
Yace ya yanke shawarar janyewa bayan shawara da kwamitin kamfensa kuma kawo yanzu sun samu N83.2 million sakamakon gudunmuwa daga wajen masoya.
Ya kara da cewa zai maida musu kudadensu.
Yace:
“A fahimtarmu wannan abu (tsadar kudin fom) zai mayar da siyasarmu wajen cin kasuwa, zai halasta sayen kuri’u, zai kara yawan rashawa da kuma kawar da matasa daga shiga siyasa.”
“Lokacin da ya muka bayyana fahimtarmu wa yan jarida, jam’iyyar tace an yi tsadar Fam ne don sanin wadanda da gaske suke ku wasa.”
Adamu Garba.
-
News3 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News5 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
