Connect with us

News

WANI SAURAYI YAYI MURNAR ZAGAYOWAR SHEKARARSA A MAKABARTA.

Published

on

Daga Khadija Abdullahi Mahmud.

 

 

Wani matashi ya kara shekara daya a rayuwarsa don haka ya yanke shawarar raya wannan rana a makabarta

A wani bidiyo da ke yawo a shafukan soshiyal midiya, an gano uban taron da abokansa suna shakatawa a tsakakkanin kaburbura.

Dukkanin wadanda suka halarci taron sun kasance sanye da fararen tufafi yayin da suka dunga daukar hotuna don tarihi.

Advertisement

A bidiyon wanda shafin @cocoacitytv ya wallafa a dandalin TikTok ya nuno mahalarta taron suna shakatawa a tsakakkanin kaburbura.

An daura kek din a kan wani teburi bayan an lullube shi da farin kyalle da lemuka iri-iri jere a kansa.

Jama’a da dama sun cika da al’ajabin dalilin da zai sa uban gayyar ya zabi makabarta domin raya wannan rana.

“Sun yi sa’a makabartan na a cikin gari ne don haka suka wataya, inama ace wannan taron a makabartar wasu kauyuka aka yi.. da an ga gudun fanfalaki.”
priscillaaryee702gmail.0 ya ce:

“Idan ka tuna ranar haihuwarka toh dole ka tuna ranar mutuwarka, hakan ya yi kyau dan uwa da ku tuna cewa suma kamar mu ne.”
AMADI ASARE ya ce:

“Ina ganin ya kamata mu dunga tambayoyi kamar, shin yana da kyau cin abinci a makabarta ko babu kyau? Muna iya tambayan kakanni da iyayenmu.”

Advertisement

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending